Alhamis 2 Yuli 2026 - 18:50
Yarjejeniyar Washington: Gawa Wadda Ke Share Fagen Rarrabuwar Kasar Lebanon

Hauza/ Bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar sasantawa ta kai-tsaye tsakanin gwamnatin Lebanon da gwamnatin Sahayoniya ta Isra'ila karkashin kulawar Amurka, wata babbar igiyar fushi da adawar bangaren siyasa da na al'umma ya mamaye daukacin kasar Lebanon; inda jam'iyyu masu zaman kansu da magoya bayan gwagwarmaya (Mukawama) suka bayyana wannan yarjejeniya a matsayin gawa wadda ke share fagen rarrabuwar kasa da yakin cikin gida.

Kamar yadda rahoton sashen kasa da kasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga Beirut ya nuna; a daidai lokacin da al'ummar Lebanon da ake zalunta, musamman a yankunan kudancin kasar, ke fuskantar hare-haren wuce gona da iri a kullum daga Sahayoniya kuma suke fuskantar mawuyacin halin gudun hijira, sanya hannu kan yarjejeniyar baya-bayan nan tsakanin gwamnatin Lebanon da Tel Aviv ya hadu da gagarumar adawa da ba a taba ganin irinta ba. Wannan yarjejeniya ba wai kawai ta hadu da tsauraran adawa daga mabiya Shi'a da magoya bayan Hizbullah ba ne, a'a, har ma da kungiyoyin siyasa daban-daban da na Kiristocin Lebanon sun bayyana ta a matsayin takarda mai hatsari ga ikon kasar.

Gargadin Shugabannin Siyasa: Wannan Yarjejeniya Shiri Ne Na Rushe Hadin Kan Kasa

A cikin wannan tsari, manyan jami'ai da sakatarorin kungiyoyin siyasa na Lebanon, yayin da suke zantawa da kafafen yada labarai, sun bayyana hatsarin da ke tattare da wannan yarjejeniya:

Hanna Gharib (Sakataren Koli na Jam'iyyar gurguzu ta Lebanon - Communist): Yayin da yake sukar dukkan wani shiri na daidaita alaka da yan mamaya, ya jaddada cewa: "Al'umma mai daraja ta Lebanon ba za ta taba amincewa da yarjejeniyar da za ta raunana ikon kasa da tabbatar da mamaya ba."

Ihab Hamadah (Dan Majalisa kuma memba a kungiya mai biyayya ga gwagwarmaya): Hamadah, yayin da yake nuni ga matsayi mai karfi na Nabih Berri, Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon, ya bayyana cewa: "Babban burin wannan tsari na bangarori uku (Gwamnati, Makiya, da Amurka), shi ne haifar da fitina da tura 'yan Lebanon fada da juna domin tabbatar da tsaron gwamnatin Sahyoniya. Wannan takarda an haife ta ne a matsayin gawa, kuma gwamnati ba ta da ikon mika ko da kwayar yashi daya na kasar nan."

 Najah Wakim (Wanda ya kafa kungiyar Harakatup Sha'ab): Wakim, bayan ganawarsa da Nabih Berri a Ain al-Tineh, ya bayyana wannan yarjejeniya da cewa ta fi hatsari nesa ba kusa ba fiye da yarjejeniyar kaskanci ta 17 ga Mayu, 1983, inda ya ce: "A wancan lokacin burin shi ne janyo Lebanon zuwa ga zaman lafiya na dole, amma a yau babban burin Amurka da Isra'ila shi ne rarraba Lebanon gaba daya ta hanyar dorawa sojoji nauyin tsaro da kuma tura kasar zuwa ga yakin cikin gida wanda zai lalata komai."

Matsalolin Dan Adamtaka; 'Yan Gudun Hijira Miliyan Daya Amma Masu Alfahari

An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a daidai lokacin da, kamar yadda Imran Riza, mai gudanar da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon ya sanar, sakamakon hare-haren Isra'ila na ci gaba, kusan mutane miliyan 1 sun zama 'yan gudun hijira a kasar, sannan mutane miliyan 1.4 suna bukatar agajin jin kai na gaggawa.

Duk da haka, rahotanni da tattaunawa ta zahiri da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya yi da mabiya Shi'a da wasu 'yan gudun hijira na kudancin Lebanon sun nuna cewa ruhin gwagwarmaya yana nan da karfinsa. Magoya bayan gwagwarmaya sun jaddada cewa: "A shirye muke mu jure wahalhalun gudun hijira da yaki, amma ba za mu taba amincewa da kaskanci, yin shiru, da tsagaita yaki na bangare guda ba; wanda hakan ke barin hannun makiya a bude wajen kashe matasanmu ba tare da muna da damar mayar da martani ba."

Shekaru Arba'in Na Juriya; Gwagwarmaya Ita Ce Garkuwar Lebanon Mai 'Yanci

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a Lebanon, a cikin shekaru arba'in da suka gabata, ta hanyar gabatar da mafi girman sadaukarwa da shahidai, ba ta taba barin ko da takun tafi daya na kasar nan ya kasance karkashin mamayar Sahyoniya ba. Hizbullah ta rubuta mafi girman misali na sadaukarwa ta hanyar mika jini mai tsarki na Shahid Sayyid Hassan Nasrullah ga al'ummar Musulmi; shugaban da ya sadaukar da daukacin rayuwarsa, magoya bayansa, da mayakansa wajen yaki da makiya na waje da kuma 'yan koren cikin gida, kuma bai taba barin Lebanon ta zama filin yakin cikin gida ba.

A yau ma, Sabon Sakataren Hizbullah da mayakan gwagwarmaya waɗanda suke sadaukar da rayuwarsu, tare da cikakken goyon bayan al'umma, sun sake gina garkuwa mai karfi a gaban wannan makarkashiya ta Amurka da Sahiyoniya, kuma ba za su taba barin kasa mai tsarki ta Lebanon ta zama filin cin kazar makiya ko fitinar cikin gida ba.
 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha